TARIHIN JAHAR KATSINA KASHI NA DAYA DAGA MAGABATA
KOKOWAR SANAU DA KORAU-zamanin mulkin habe,sarautar katsina gasarta ake yi ta hanyar kokowa,wadda akan yi kowace shekara.Duk wanda yake so ya hau gado,sai ya ja da sarkin da yake akai.Idan yayi nasara sai ya yanka shi,sannan ya hau karagar mulki.Idan kuwa shi aka kaya,to sai sarkin mai ci ya yanka shi.
A lokacin irin wannan kokowar saurata ce ta shekara-shekara,korau ya ja da sarki sanau.shi korau kamar yadda muka samu labari ance. wani shaharerren dan kokowa ne da ya fito daga garin 'yandoto.wasu kuma sun ce malami ne daga wannan garin ya je durbi ta kusheyi domin kira ga addinin musulunci.To akan haka ne ya zama malamin sarki jibda yaki sanau,wanda ya yaudara ya kashe.
copyright © 2017-2018 ,Shafin musawa
Alright reserved